Amirul Hajj na Jahar Filato, Mai martaba sarkin Kanam, Alhaji Muhammadu Mu’azu na biyu yace maida dukkan shirye-shiryen aikin haji da gwamnatin tarayya tayi zuwa hukumar alhazai ta kasa, shine ke janyo matsala.
Jagoran malamai da zasu karantadda mahajjatan Jahar Filato a kasa mai tsarki, Sheik Aminu Yusuf Nuhu yace ya dace a dauki matakan gyara don kaucewa matsalar kwashe maniyyatan.
A bangaren hukumar alhazai ta kasa, a wata sanarwa daga daraktan hulda da jama’a na hukumar, Hajiya Fatima Usara, ta bayyana rashin jin dadinta, na kasa kwashe maniyyatan zawa kasa mai tsarki.
Sanarwar ta nemi ahuwar gwamnatin tarayya, hukumomin jin dadin alhazai na jihohi, kamfanoni masu zaman kansu dake jigilar alhazai, da sauran jama’a.
Sanarwar ta kuma jaddada cewa zata mayar wa dukkan maniyyata da basu sami tafiya ba kudadensu.
Ta kuma ce zata yi aiki tukuru don tabbatar da ganin ba’a sami matsala a aikin hajjin badi ba.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5