A cigaba da fafatawar da kungiyoyin ‘yan wasan nahiyar Afirka ke yi na shiga gasar cin kofin wasannin kwallon kafa na nahiyar wanda ake bugawa a Ruwanda , Mali ta lallasa Ivory Cost da ci 1-0.
Yves Bissoounma ne ya jefa kwallon wadda Hamidou Sinayoko ya gyara masa da kai a cikin mintuna 88 da aka kwashe ana fafatawa.
A zagayen farko na wasan, Essis Aka ya kai wani gagarumin hari amma sai kwallon ta daki karfen mai tsaron gida ta kauce.
Mali zata hadu da jamhuriyar demokaradiyyar Kongo a wasansu na karshe ranar lahadai idan Allha ya kaimu wanda za’a buga a Kigali.
Daga karshe wasan ya tashi ne a yayin da dan wasan Malin ya jefa kwallon bayan wasan kurar da yayi tsakanin ‘yan wasan na Ivory Cost sa’an nan ya jefa kwallon a raga.
Koda shike akwai abu guda da bai yi wa Malin dadi ba, wato dan wasanta guda Sekou Diara da alkalin wasa ya dakatar dan haka bazai kasance a wasan da kasar zata buga da jamhuriyar demokaradiyyar Kongo ba.