Ministan tsaro na kasar Amurka Mr. Ashton B. Carter, ya bayyanar da wani sabon tsare-tsare nasu, wanda zai kawo karshen matsalar rashin haihuwa ko mace-mace da tayi yawa a cikin rundunar sojojin kasar. Yace sojoji da dama maza da mata, sun samu nakasa da bazata basu damar haihuwa ba a iya tsawon rayuwar su, sanadiyar harbi ko tashin boma-bomai da ya nakasa su, a lokacin yakin kasashen Iraq da Afghanistan.
Yace yin hakan zai kara sa matasa su shiga aikin soja, domin kuwa kafun su tafi za’a diba ruwan kwayayen halittar dan'adam na haihuwa daga jikin su “Spam” na namiji ko mace, sai a saka shi cikin wani ma’adani da zai ajiye shi tsawon shekaru da dama. Wanda daga bisani idan mutun ya dawo daga yaki a kowace kasa kuma yasamu nakasa da baza su iya haihuwa ba, sai kawai a dakko wannan ruwan maniyin nasu a sakashi a jikin masoyan su sai su samu haihuwa.
Duk kuma maccen da ta kwashe shekaru 10 tana aikin soji, zata iya bari sai ta koma gida don neman haihuwa. Wasu manyan kamfanoni na nan kasar Amurka kamar su Facebook, har sun bada tasu gudun mawar kudi da suka kai dallar Amurka $10,000 dai-dai da naira 2,000,000, don ajiye wannan kwayayen halitun. Ganin cewar wannan hukumar ta Pentagon itace hukumar da tafi kowace hukuma ma’aikata a fadin duniya. Masu sharhi na ganin cewar da sake, domin kuwa ajiye kwayoyin halittar dan’adam nada banbanci da ajiye kaza ko kifi a cikin firij.