Tafiyar da bata wuce nisan Kano zuwa Kaduna ba, ta dauki wata wasika shekaru 60. A watan Afrilu na shekarar 1952, wani fursunan siyasa Guo Ching, dan kasar Taiwan, ya rubuta wasika zuwa ga iyalanshi wanda yake yi musu bankwana, domin yana da masaniyar cewar an yanke mishi hukuncin kisa.
Bisa wannan dalilin, ya rubuta wannan wasikar ya kuma aika da ita ga iyalan shi da suke wani gari. A dai tsakanin shekarun 1947 zuwa 1987 gwamnatin mulkin gurguzu ta kasar Taiwan, tayi wa mutane sama da 1,000 hukuncin kisa bisa zargin su da akeyi na suna yima gwamnatin kasar China, munafurci game da kasar. Kana da wadan su ‘yan siyasa da suke adawa da gwamnatin a wannan lokacin. Akwai dai wasiku sama da 177 da mutane suka rubuta ma iyalan su, amma a wancan lokacin gwamnatin kasar bata bada wasikun ga wadanda aka rubuta don su ba.
A dai-dai lokacin da ‘yar wannan mutumin Guo Su-jen, ta samu wannan wasikar, tana da shekaru 60, ta nuna alhinin ta dangane da hukuncin da akayi ma mahaifin nata, da kuma yadda wannan wasikar bata kai gare suba sai a wannan lokacin. Ta bayyanar da cewar tayi kuka matuka, domi kuwa bata san mahaifinta ba, amma ta wannan wasikar tana ganin kamar cewar har yanzu yana raye. Kana wannan rubutun na mahaifin ta, ya bayyanar mata da ya kamannun shi suke. Sabuwar shugaban kasar da aka zaba ta dau alwashin kawo canji a kasar mai ma’ana.