Mali Ta Ce Ba Za Ta Mutunta Wa'adin Jiran Shekara Ba Na Janyewa Daga ECOWAS

Shugaban sojojin Mali Assimi Goita

Kasar Mali ta fada a ranar Laraba cewa, ba za ta jira shekara guda kafin ta fice daga kungiyar ECOWAS ba, kamar yadda yarjejeniyar kungiyar ta bukata.

WASHINGTON, D. C. - Kasar ta Mali da makwabtanta Nijar da Burkina Faso, wadanda ke karkashin mulkin sojoji, sun sanar a watan da ya gabata cewa, nan take za su fice daga kungiyar ECOWAS, babbar kungiyar siyasa da bunkasa tattalin arziki a yammacin Afirka, lamarin da ya kawo koma baya ga yankin dake a hade na tsawon shekaru da dama.

ECOWAS

Dukkanin kasashen uku sun sanar da hukumar ta ECOWAS matakin da suka yanke na ficewa daga kungiyar a rubuce ne a ranar 29 ga watan Janairu, wanda a cewar yarjejeniyar za su ci gaba da zama mamba har sai shekara guda daga ranar.

A cikin wata sanarwa da ta wallafa ta yanar gizo, ma'aikatar harkokin wajen kasar Mali ta ce kungiyar ECOWAS ta keta ka'idojinta ta hanyar rufe iyakokinta da kasar Mali a lokacin da ta kakaba wa gwamnatin sojan kasar takunkumi.

Mali

Sanarwar ta ce, "Saboda haka, gwamnatin Jamhuriyar Mali ba ta da iyaka nauyin daukaka wa'adin da aka ambata a cikin sashe na 91 na yarjejeniyar da aka yi wa kwaskwarima."

Ma'aikatar harkokin wajen kasar da hadin gwiwar ta kasa da kasa ta nanata matakin da gwamnatin kasar Mali ta dauka na ficewa daga kungiyar ECOWAS ba tare da bata lokaci ba, sakamakon take hakkin kungiyar akan ka’idar da ta rubuta nata, da kuma wasu dalilai na halal.

SOJOJI A MALI

Kawo yanzu dai babu wani martani daga kungiyar ECOWAS, ko kuma daga kasashen Nijar da Burkina Faso kan ko za su bi sahun hakan. Kungiyar ECOWAS dai ta shirya wani taro a ranar 8 ga watan Fabrairu domin tattauna lamarin.

Ficewar kasashen uku dai koma baya ne ga kungiyar kasashen 15 da ke kokarin tattaunawa da shugabannin sojojin domin maido da mulkin dimokradiyya.

-Reuters