WASHINGTON, D.C. — Wannan shi ne karo na biyu da guguwar ta Freddy take ratsawa ta kudancin nahiyar cikin wata guda a karshen mako kuma har yanzu tana haifar da ruwan sama mai karfi a ranar Laraba, wanda ke kawo cikas ga ayyukan agaji.
Ma'aikatar kula da bala'o'i ta Malawi a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce adadin wadanda suka mutu a ibtila’in na biyu ya kai 225, daga 190 a ranar Talata, inda mutum 707 suka jikkata, yayin da 41 suka bata.
A makwabciyar kasar Mozambique, akalla mutane 21 ne suka mutu ya zuwa ranar Talata, a cewar hukumomi.
Adadin wadanda suka mutu tun lokacin da guguwar ta Freddy ta fara sauka a watan Fabrairu yanzu an kiyasta fiye da 270 a Malawi, Mozambique da Madagascar.
Sojojin Malawi da 'yan sanda da kungiyar agaji ta Red Cross da sauran kungiyoyin agaji na gudanar da aikin bincike da ceto, inda cibiyar kasuwanci ta Blantyre na daya daga cikin wuraren da aka fi fama da matsalar.
Ambaliyar ruwa mai tsanani da zabtarewar laka sun yi awon gaba da gidaje tare da karya gadoji da lalata hanyoyi.
Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya ci gaba da afkawa tashar ruwan Quelimane na Mozambique da kewaye.
"Muhimmancinmu a yanzu, yayin da muke la'akkari da alhinin abin da ya faru, shi ne bincike da ceto mutane a mafi yawan wuraren da suka lalace. Mun ceto dubban mutane amma har yanzu ba a iya kaiwa ga wasu dubbai ba," Kakakin hukumar agajin gaggawa Paulo Tomas ya fada daga Quelimane.
-Reuters