Makomar ‘Yan Kasashen Afirka Bayan Dokar Hana Shiga Nijar Ba Tare Da Takardu Ba

Shugaban mulkin sojan Nijar Janar Abdourahamane Tiani

‘Yan kasashen Afirka kamar Najeriya dake gudanar da harkokin kasuwanci a Nijar sun bayyana damuwa game da matakin gwamnatin mulkin sojan kasar na kafa dokar haramta wa 'yan kasashen waje shiga Nijar ba tare da takardun bulaguro ko na izinin zama ba

Yanzu haka dai akwai dubban ‘yan tarayyar Najeriya dake gudanar da harkokinsu na yau da kullun a Nijar, to sai dai samar da wannan dokar za ta haifar da matsala a tsakanin al’ummomin da ke son shiga Nijar gudanar da harkokinsu.

Dokar za ta fi shafar 'yan Najeriya ganin irin dangantaka ta shekaru aru-aru da ke tsakanin kasashen biyu, to sai dai ‘yan Najeriya da ke zaune a Nijar na ganin akwai bukatar tattaunawa tsakanin gwamnatin tarayya da kuma hukumomin mulkin sojan kasar Nijar domin sanin makomar ‘yan kasashen da ke rayuwa a Nijar.

Barazanar kutse a yunkurin ta da hargitsi da gwamnatin Nijar ke zargin wasu kasashen ketare da hannu shi ne mafarin bullo da wannan doka abin da wasu ‘yan Najeriya ke ganin abu ne mai kyau daukar irin wannan matakin domin tsare kasa.

Masana dai na ganin wannan dokar ta kara fayyace abin da ficewar Nijar daga ECOWAS ke nufi, don haka acewarsu wannan dokar ba za ta shafi kai kawon jama’ar kasashen ECOWAS ba da dukiyoyinsu tun da a baya kasashen AES a wata sanarwa da suka fitar sun tabbatar da cewa ficewarsu daga ECOWAS ko CEDEAO ba za ta shafi ‘yan zirga-zirgar mutanen kasashen ba, ba tare da biza ba.

Saurari cikakken rahoto daga Hamid Mahmud:

Your browser doesn’t support HTML5

Makomar ‘Yan Kasashen Afirka Bayan Dokar Hana Shiga Nijar Ba Tare Da Takardu Ba.mp3