Kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma (ECOWAS) ta bayyana zarge-zargen ta'addancin da jamhuriyar Nijar ke yiwa Najeriya da wasu kasashe mambobinta da marasa tushe, inda tace tana bayan mambobin nata.
Jamhuriyar Nijar ta zargi Najeriya da mambobin ECOWAS da hada baki da kasar Faransa da nufin hargitsa kasar.
Sai dai sanarwar da ECOWAS ta fitar a jiya Alhamis ta bayyana zarge-zargen da "marasa tushe."
"Hukumar gudanarwar ECOWAS na bayyana matukar damuwa a kan zarge-zargen da ake yiwa Najeriya da wasu kasashe mambobinta.
"A kan haka, ECOWAS ke musanta duk wani zargi dake danganta wannan babbar kasa mai karamci da daukar nauyin ayyukan ta'addanci," a cewar wani sashe na sanarwar.
Don haka ECOWAS ke kira ga dukkanin mambobinta da ke yankin da su dabbaka akidar tattaunawa da juna da zaman lafiya tare da kaucewa zarge-zarge marasa hujja.
A jiya Alhamis gwamnatin tarayyar Najeriya ta musanta zarge-zargen da jamhuriyar Nijar ta yi.
Babban Ministan Tsaro Badaru Abubakar ya bayyanawa wakilin Muryar Amurka, Umar Farouk Musa a Abuja cewa yana cikin tawagar Shugaba Tinubu a dukkan ziyarar da Shugaba Bola ya kai Faransa kuma babu lokacin da aka yi maganar girke sojojin Faransa ko basu sansani a Nigeria.
Saurari cikakken hirar Babban Ministan Tsaro da Umar Farouk Musa
Dandalin Mu Tattauna