Sanarwar wace ministan harakokin wajen Mali, Abdoulaye Diop ya gabatar ta kafar talbijan Ortm dauke da sa hannun shugaban rikon kungiyar confédération AES, Janar Assimi Goita, ta fara da tunatarwa kan kafuwar kungiyar da makasudun kafa ta.
Sanrawar ta kara da cewa kasancewar su masu mutunta dokoki da manufofin MDD (Majlisar Dinkin Duniya) da dokokin kungiyar Tarayyar Afirka AU, kasashen na AES sun ce la'akari da dan uwantaka da zumunci da alaka da a wani bangaren, hada kan al'umomin Afrika, ya sa Mali, Nijar da Burkina Faso yanke shawarar bai wa jama'ar kasashen ECOWAS izinin shiga ko zama a yankin AES ba tare da bukatar takardar bisa ba, amma kuma da sharadin mutunta dokokin kowacce daga cikin wadanan kasashe.
Ya kuma bayyana cewa kasashen na AES na da ‘yancin kin yarda da bakuntar dan yankin ECOWAS da dokokin kasashen 3 ke dauka a matsayin bakon da bai cike sahrudan samun cikakiyyar yarda ba.
A tattaunwar shi da wakilin Muryar Amurka a Ni'amey Souley Moumouni Barma, masani kan huldar kasa da kasa Moustapha Abdoulaye, ya ce ya yiwu kasashen na AES Sahel, sun dau wannan mataki ne don kaucewa samun wata baraka.
Nijar, Mali da Burkina Faso da yanzu suke karkashin mulkin soja, sun fice daga kungiyar ECOWAS a ranar 28 ga watan janerun 2024 sakamakon zargin kungiyar da kauce wa ainahin manufofin kafa ta.
A latsa nan domin sauraron rahoton Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna