Makirci Aka Shiryo Dan Kawoma Shugaba Buhari Cikas

Shugaba Muhammadu Buhari

Har yanzu barakar da ke Jamiyyar APC akan batun zaben shuwagabani a Majalisar Wakilai na kara Kamari.

Masu goyon banyan Kakakin Majlisar Yakubu Dogara, da suke kiran Kansu Equity Group, sun ce an yi sulhu.

Sun bayan haka ne a wani taron manema labarai da suka kira a Abuja, inda Abdulmumini Jibrin, ya zayyana yadda aka raba mukaman, yace “ Alhassan Ado Doguwa, daga jihar Kano arewa maso yamma, a matsayin jagoran Majalisa, Buba Jibrin, daga jihar Kogi, arewa ta tsakiya, a matsayin mataimakin jagoran Majalisa, Pally Iriase, daga jihar Edo, kudu maso kudu a matsayin mai tsawatawa da kuma Chika Okafor daga jihar Imo kudu maso gabas a matsayin mataimakin mai tsawatarwa.”

Magoya bayan Femi Gbajabiamila, wadanda su kuma ke kiran kansu Loyalist Group sun ce ba haka zancen yake ba Ahmed Babba Kaita, yace “ Zamu koma zauren Majalisa ranar Talata kuma muna sa ran idan an bi dokokin Majalisa da yadda tsarin doka yake na cikin Majalisa, a fito ‘ya’yan jamiyyar APC, suje suyi zabe idan anyi wannan zabe duk wanda Allah yaba, damu dasu ‘yan bayan Dogara, muna sa ran za’a samu zaman lafiya idan har ta tabbata cewa an bi wandannan ka’idojin tsoron ‘yan Majalisa shine abinda ya faru a Majalisar Dattijai inda Saraki ya zauna ya kira sunayen mutane yace sune ya ki bin abun da tsarin dokokin tafiyar da Majalisa yace.”

Babba Kaita, ya kara da cewa wani makirci ne aka shiryo na yin kaka gida a zaurukan majalisun domin a shigo ma jamiyyar APC, da kuma kawo cikas ga shugaba Muhammadu Buhari, a majalisa.

Daga dukkan alamu APC, na da sauran aiki a kokarinta na daidaita tsakanin ‘ya’yan nata da nufin samar da shugabanci mai dorewa.