WASHINGTON, DC —
Rahotani daga jihar Yobe, na nuni da cewa an samu tashin wani bom a wajen binciken ababen hawa wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane hudu da raunata wasu da dama.
Wannan tashin bom din dai yazo ne kwana daya bayan sanarwar da Hafsan Sojojin kasar Manjo Janar Tukur Buratai, yayi na canja sunan rudunar dake fafatawa da ‘yan kungiyar Boko Haram, daga “ Operation Zaman Lafiya zuwa Operation Lafiya Dole.”
Wannan tashin bom din dai ya afku ne daf da shiga garin Damaturu inda jami’an ‘yan Sanda ke binciken motoci, rahotanin na c gaba da cewa maharani sun zo ne cikin wata mota, suka kuma tada bom din a dai dai lokacin da jami’an ‘yan Sandan ke kokarin bincikan takardun motar su wanda aka ce ya tashi dasu dama maharani dake cikin motar.