Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilin Faduwar Darajar Naira a Kasuwar Kudi


An danganta faduwar darajar Naira akan faduwar farashin gurbatancen man a kasuwar duniya, wani masanin tattalin arzikin kasa Alhaji Shuaibu Idris Mikati, wandan kuma ya taba takarar neman mikamin Gwamna a jihar Kaduna, ne ya furta haka a wata hira da abokin aikin mu Ladan Ayawa.

Yace “kasuwar man fetur yayi kasa, shekaru kamar goma shabiyar dasuka wuce an baiwa Gwamnatin Najeriya, na wannan lokacin wato Gwamnatin shugaban kasa Obasanjo, shawarar cewa kasar Amurka, ta gano wani lungu da zata iya samu mai, kuma idan ta samu man nan ta fara hako shi farashin mai a duniya, zai yi kasa saboda haka yakamata Najeriya, ta fara tunanin yin tattalin a lokacin da take wadatar kudi”

Ya kara da cewa shugaba Obasanjo, ne ya fara kawo wani salon a ajiye kudin rarar man da ake saidawa inda aka tara kudi kimanin Dala miliya dubu 67,000, baya tara wadannan kudade Gwamnatoci da suka biyo baya sai suka fara rabe raben kudin ana kashewa kamar gobe bazata zo ba.

Yana mai cewa yau sai gashi farashin man da ake saidawa dala 110, yau ganga bata wuce dala 55, idan kudin shiga da ake samu ya ragu kuma aka ci gaba da kashe kamar yadda aka saba dole kasa ta samu matsala, toh abun da ya sami Najeriya, kennan shi yasa dole darajan Naira , tayi kasa.

XS
SM
MD
LG