Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bankin Duniya ya Bama Gwamnatin Buhari Gudunmawar $2.1


Zuwan shugaban kasa Muhammadu Buhari Amrka
Zuwan shugaban kasa Muhammadu Buhari Amrka

A wata ganawa da shugaban kasa Muhammadun Buhari yayi da shugaban babban Bankin Duniya, a gidan alfarma na shugaban kasar Amurka jiya, shugaban banakin duniya ya mika kyautar gudunmawar babban bankin duniya ga shugaba Muhammadu Buhari.

Da zummar gina jihohin yankin gabas maso yamma, da suka fuskanci tashin tashina a yankin, tundaga shekarar 2009 zuwa yanzu. Shugaban bankin dai yace, sun bada wannan gudun mawar ne domin su tallafawa sabuwar gwamnati ta Muhammadu Buhari, don su samu su aiwatar da ayyukan gina kasa, da kuma kiwon lafiya, samar da aikinyi ga matasa a yankin da rikicin Boko Haram ya addaba.

A wata tattaunawa da dandalin VOA yayi da Dr. Aliyu Pate, tsohon ministan lafiaya a Najeriya, wanda ya jagoranci tawagar ta Bankin duyia da suka gana da shugaba Muhammadu Buhari, yace bankin duniya sun bama sabuwar gwamnatin gudunmawar dalar Amrka biliyan biyu da miliyan daya $2.1

Babban burinsu shine a maganje matsalar boko haram a yanki, kana matasa su samu abubuwanyi domin wadannan ‘yan ta’addan na amfani da wannan dammar ce ganin matasa basu da abun yi, su sasu cikin wannan muguwar dabi’ar. Don haka suna fatar za’ayi amfani da wannan kudin wajen aiwatar da wanna aikin batare da bata lokaciba. Duk acikin wannan tattaunawar wakilan gidauniya mai kudinnan na duniya wato Bill Gate, suma sun gana da shugaban kasar inda suka nuna nasu yunkurin na taimakama sabuwar gwamnatinshi don ta samu nasara.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG