Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasa Ina Basirar da Allah Yabaku


Matashi Mai Limozin da Jirgin ruwa
Matashi Mai Limozin da Jirgin ruwa

Idan har baku manata da tattaunawarmu da matashinan da’ake masuna Ofisa ba, wanda yake kirkirar motoci, gidaje, da dai abubuwan more rayuwa na yau da kullun. Yauma yayi muna karin bayani dangane da sabuwar motar Limozin da jirgin ruwa da kera, kuma ya yimusu suffa da tsari irin yadda na gasken suke.

Yanzu dai yana kokarin samusu ingina ne wadanda zasu sasu suyi aiki kamar na gaske, yadai sama ita wannan motar ta alfarma duk abubuwanda ta gasken take da kujeru irin na alfarma da kayan shakatawa, wanda shima jirginnan na ruwa mai dauka kaya da yawa an samishi ingin.

A yanzu dai babban abun da yake ganin yakamata yayi shine ya koakrta wajen ganin ya inganta kir-kire kir-kirenshi, wanjen samar da duk kayan da suka kamata masu nagarta, don kuwa yana da tabbacin cewar samar da waddannan kayan su zasu sa basirarshi ta karu, da kuma kokarin kara jawo hankalin wasu matasa suma suyi sha’awar bayyanar da tasu fahimtar a fili.

Wai ina matasa masu hazaka, da basira da Allah, yabaku kuzo ga dama tasamu, duk wanda yasan yana da wata basira da zai nunama ‘yan’uwanshi matasa to yaje shafinmu na Dandalin VOA a facebook ya aiko muna da sako, zamu kirashi domin tattaunawa dashi.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG