Majalisar Wakilai Ta Umarci CBN Ya Dakatar Da Shirin Kayyade Kudaden Da Za A Cire Banki

Lokacin da Buhari yake gabatar da kasafin kudin 2022 a gaban majalisar dokoki ((Facebook/Femi Adesina))

Lokacin da Buhari yake gabatar da kasafin kudin 2022 a gaban majalisar dokoki ((Facebook/Femi Adesina))

Hakazalika, Majalisar ta kuma umarci Gwamnan Babban Bankin na CBN Godwin Emeifele,  da ya bayyana a gabanta a ranar Alhamis mai zuwa.

Majalisar Wakilai ta bukaci Babban Bankin Najeriya CBN da ya dakatar da aiwatar da sabon tsarin da ya kirikiro, wanda zai takaita adadin kudin da za a iya cirewa a banki.

Shirin zai fara aiki ne a ranar 9 ga watan Janairu, 2023.

Hakazalika, Majalisar ta kuma gayyaci Gwamna Babban Bankin Godwin Emeifele kamar yadda dokar babban bankin kasa ta tanada domin ya yi wa majalisar bayani kan tsare-tsaren da bankin ya ke aiwatar a ‘yan kwanakin nan.

Sabuwar manufar Babban Bankin dai ta kayyade cire N20,000 a kullun da kuma N100,000 a mako.

Mambobin majalisar sun nuna fushinsu a yau Alhamis, yayin da ‘yan majalisar ke bi da bi suna yin Allah wadai da sabon tsarin cire kudaden, suna masu cewa hakan zai yi matukar shafar kanana masana’antu da tattalin arziki, tun da galibi al’ummomin karkara ba su da damar yin harkar banki.

Sai dai bayan wani batu da Mk Gbillah ya gabtar kan tanade-tanade, babban babban bankin kasar, majalisar ya umarci Gwamnan CBN da ya gurfana gabanta a ranar Alhamis, 15 ga watan Disamba, 2022 domin yi wa majalisar bayani.

Wanda ya gabatar da kudurin, Magaji Da’u Aliyu, ya ce sabuwar manufar babban bankin ta CBN ya fitar na kayyade yawan kudaden da za’a rika fitar wa a kullun zuwa N20,000 a kullun bai kamata ba, domin hakan zai yi illa ga al’ummar Najeriya, musamman masu gudanar da kananan sana’o’i.