Majalisar Somaliya Ta Amince Da Wasu Sauye Sauye A Kundin Tsarin Mulkin Kasar

Hassan Sheikh Mohamoud

Majalissar dokokin kasar Somaliya ta amince da sauye-sauyen kundin tsarin mulkin kasar jiya Laraba wanda zai yarda majalissar ta cigaba da ayyukanta ko da shugabannin kasar sun kasa gudanar da zaben kasar wanda ake shirin yi.

Matakin majalissar ya kara karfafa zaman dar-dar da ake na cewa watakila karshenta ma ba za'a gudanarda zaben ‘yan majalissar ba a watan Agusta da kuma na shugaban kasa da za a yi a watan satunba. Daman dai shugabannin kasar sun dan makara wajen amincewa da cikakken bayanan shirin zaben, da kuma matsayin babban birnin kasar (na ko zai ci gaba da zama babban birnin kasar ko a maida shi wata jiha), da kuma yin garambawul ga tsarin kundin mulkin kasar wanda zai amincewa hukumomin gwamnatin kasar gudanar da ayyukansu ko bayan sun gama wa’adinsu.
Daraktan Cibiyar binciken Sahan, mai sharhi kuma akan lamura a yankin, Matt Bryeden ya fadi cewa shugabannin zasu iya gudanar da zaben kasar bisa lokaci don cigaban gwamnatin kasar.
Bryden yayi gargadi akan jinkirta ko dage zaben, abinda ‘yan kasar da yawa ke fargaba.