A Nijar, hukumomin kasar sun ce sun gano gawarwakin mutane 34, inda 20 daga cikinsu yara ne da suna kokarin ketare hamada.Jami'an gwamnati suka ce sun hakikance mutanen 'yan ci rani ne da suka doshi arewa da fatan su kai Aljeriya, ko kuma Turai.
Ma'aikatar cikin gidan kasar ce ta bada wannan sanarwar gano gawarwakin jiya Laraba. A cikin bayanin da aka yi a tashar talabijin tace mata tara da maza biyar da yara 20 din sun mutu ne sakamakon kishin ruwa,bayan da masu safarar mutane suka yi watsi da su a hamada.
Har yanzu ba'a tantance ko mutanen 'yan wace kasa ba ne. Kungiyar kula da 'yan gudun hijira ko ci rani ta kasa da aksa tace adadin masu irin wannan tafiye tafiyen ya karu sosai daga yankunan da suke kudu da hamadar sahara zuwa Turai, musamman daga kasashe da suke yamma da kuma Afirka ta Tsakiya.