Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fada Ya Barke Tsakanin Sojojin Gwamnati Da Wata Kungiya A Sudan Ta Kudu


Sojojin Sudan Ta Kudu
Sojojin Sudan Ta Kudu

Akwai fargaban cewa mutane da yawa sun mutu bayan da wani fada ya barke jiya Laraba, tsakanin dakarun gwamnati da mayakan wata kungiyar ‘yan bindiga da ba sannaniya ba a garin Raja dake sabuwar jihar Lol dake kasar Sudan ta Kudu.

Wani shugaban chochi na yankin ya ce mutane fiye da 400 sun tsere zuwa wata chocin Katolika dake garin. Wasu daga garin na Raja sun ce gwamnan jihar Rizik Zachariah Hassan da wasu mannayan jami’an jihar duk sun tsere daga wurin.
Shaidun gani da ido a garin Wau sun ce kungiyar ‘yan bindigar ta kai hari a kan sansanin sojan kasar da ke Raja, da ofishin hukumar tsaron kasar da ke kusa da kasuwar garin, da kuma gidan gwamnan jihar, tare da kashe sojoji da dama. Yawancin sauran sojojin da suka rage suma sun arce.
Fadan da aka yi a safiyar jiya ya tilastawa dumbin mutane tsarewa zuwa cin daji, yayinda wasu sauka fake a harabar chocin Katolika dake Wau a cewar shaidun gani da ido.
Magajin gari Raja Marodama James Benjamin shima yana daya daga cikin wadanda suka gudu daga garin.

XS
SM
MD
LG