Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daga Ina Boko Haram Ke Watsa Shirye Shiryensu?


A yayin da mayakan kungiyar Boko Haram suka bude kafar watsa labarai ta tashar FM mai karamin zango a jihar Arewa Mai Nisa dake jamhuriyar Kamaru.

Kungiyar Boko Haram na amfani da tashar wajen mayar da martani ga gwamnatocin da suke yakarsu, da kuma jan hankalin matasa wajen shiga ayyukan ta’addanci.

Kan wannan batu ne wakilin Muryar Amurka a Kamaru, Garba Awwal, ya nemi jin ta bakin shugaban matasa kuma dan kungiyar rajin kare hakkin bil Adama, Mallam Musa Usaini, wanda yace tabbas mutanen Kamaru sun zage dantse, domin ba zasu bari ba ayi amfani da wannan hanya wajen janyo hankalin mutane daga hanyar gaskiya zuwa hanyar ta’addanci ba.

Shima Haladu Gabdo, daya daga cikin masu bayar da shawara a hukumar harkokin cikin gidan Kamaru, ya ja hankalin jama’a da cewa duk wanda ya sani ko yaji labarin inda suke watsa shirye shiryen radiyon ya sanar da hukuma mafi kusa, kuma kada mutane suyi amfani da abinda suka ji daga wannan gidan radiyo.

Cikin kwanaki biyun da suka gaba ne maharan Boko Haram suka kashe wasu ‘yan kungiyar Kato da Gora biyu da wasu Makiyaya biyu, a gundumar Kwalfata.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:06 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG