Majalisar Dokokin Nijar Ta Amince da Kara Wa'adin Dokar Ta Baci a Jihar Diffa

Shugaba Mahamadou Issoufou na Nijar

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ce ta shigar da bukatar tsawaita dokar ta bacin a jihar Diffa wa majalisar dokokin kasar domin ta amince da karin wa'adin saboda jiha ce da 'yan Boko Haram suke yawan kai hare-haren ta'adanci

Gwamnatin ta nemi sabunta wa'adin dokar ne saboda watan jiya ne waccan dokar ta shuder bayan wata uku .

Sabunta dokar nada matukar tasiri wajen murkushe 'yan ta'adan da suke tada karin baya a yankin na Diffa.

Onarebul Hamma Asa shi ne shugaban kwamitin majalisar kasa mai kula da harkokin tsaro ya yi karin bayani. Yace dokar da aka kafa ta wata uku an ga tasirin da tayi a yankin saboda ta kare yankin tare da duk wadanda suke aiki da ita. Dare da rana jami'an tsaro na kulawa da duk wani mugu da zai shigi yankin.

Yace akwai matsaloli da suka addabi yankin Diffa kamar aika aikar 'yan kunar bakin wake da masu satar dabbobi da kuma sace mutane daga wurarensu na ainihi. Saboda haka ya zama dole gwamnati ta dauki kwararan matakai domin shawo matsalolin.

Ministan tsaron kasa Hashim Masaudu ya yabawa 'yan majalisar saboda amincewa da bukatar gwamnati. Yace duk abubuwan da suka yi a Diffa can baya da yaddar majalisa ne. Idan babu yaddar majalisa babu abun da gwamnati zata yi.Saboda haka duk wata uku gwamnati na komawa wurin majalisa ta duba lamarin da bukatar gwamnati.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Majalisar Dokokin Nijar Ta Amince da Kara Wa'adin Dokar Ta Baci a Jihar Diffa - 3' 05"