Samawa matasa aikin yi na cikin matakan da mahalarta taron da wasu kungiyoyi daga kasashen yankin tafkin Chadi suka yi akan rikicin Boko Haram da ya addabi yankinsu.
Malam Musa Cangari na wata kungiya da ta halarci taron yace kowa ya amince cewa idan har ana son a fita daga fitinar da Boko Haram ta haddasa dole ne a yi nazarin yadda za'a samarma matasa aikin yi saboda idan matasa basu da aikin yi suna iya shiga rikici.
An kuma amince a taron cewa duk abubuwan da ake yi yakamata a yi tare da shawara da jama'a da wakilansu ko sarakunan gargajiya ko wadanda suka zaba ya zamanto ana shawara ana jin maganar da mutane suke yi. Idan aka kiyaye da wadannan mataki zasu taimaka wajen shawo kan fitinar Boko Haram.
Muhammad Shuwa magatakardan kungiyar sarakunan gargajiya daga Najeriya cewa ya yi sun gamsu da shawarwarin da aka tsaya a taron kuma zasu kaiwa na gabansu labari tare da tattara jama'arsu idan sun koma gida domin su fadakar dasu.
Ga karin bayani.