Bisa al’ada kotun daukaka kara kan gabatar da irin wannan zama a kowacce shekara, domin duba hukuncin da ya dace ga mutanen da ake zargi da aikata miyagun laifuffukan da suka hada da fyade da fashi da makami da kisan kai da dai sauran laifuka.
Zaman wanda ke gudana a bainar jama’a na zaman wata dabarar fadakarwa ko hannunka mai sanda ga mutanen da suka je ganewa idanuwansu shari’ar. Sai dai kuma duk da haka bayanai na nuni da cewa jama’a na ci gaba da afakawa cikin irin wannan danyan aiki, yawanci a birane kamar yadda Alkali mai tuhuma da sunana hukuma ya bayyana a jawabinsa.
Sai dai wakilin kungiyar lauyoyi Metur Mohammed Sani Na Bara, a jawabinsa da yayi lokacin bukin bude zaman shari’ar ya bayyana cewar a sakamakon jan ran da suke fuskanta daga gwamnati kan batun mayar musu da harkokin samar da asusun kariya ga masu karamin karfi ko kananan yara. Wanda kungiyar kasashen Afirka ta Yamma renon Faransa tayi umarni ga gwamnati, lauyoyi ba zasu halarci zaman na wannan karon ba har sai an share musu hayensu.