Majalisar ta kammala aikinta a safiyar yau Alhamis bayan da tilas suka fice daga zauren majalisar na Capitol jiya Laraba, a lokacin da magoya bayan shugaba Donald Trump mai barin gado suka mamaye ginin.
Mataimakin shugaban kasa Mike Pence, wanda ya jagoranci zaman da aka katse, ya sanar a hukumace sakamako kuri’un wakilai da Biden ya samu 306, Trump kuma ya sami 232.
Trump ya shafe watannin biyu da suka shige yana ta nanata ikirari marasa hujja, na cewa shine ya yi nasara tare da kuma bukatar magoya bayansa su kalubanci sakamakon, ciki har da bayanan da ya yi jiya Laraba.
Jim kadan da majalisar ta tabbatar da nasara Biden, Trump ya yi alkawarin mika mulki cikin tsanaki a ranar 20 ga watan Janairu, “Duk da cewa ban amince da sakamakon zaben gaba daya ba.”
“A ko yaushe ina cewa zamu ci gaba da gwagwarmaya don tabbatar da cewa an kirga kuri’u na gaskiya ne kawai, “In ji Trump. “Yayin da wannan yake nuna karshen wa’adin farko mafi girma a tarihin shugaban kasa, wannan kuma shi ne na farko na fafutukar “Make America Great Again!”