Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Trump Na Ci Gaba Da Kokarin Sauya Sakamakon Zaben Shugaban Kasa


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

A wata tattaunawa ta waya ta ba sabon ba, a ranar Asabar da ta gabata, Shugaban Amurka Donald Trump, ya roki jami'an zabe a jihar Georgia su samo mashi adadin kuri’un da za su bashi damar sauya sakamakon zaben kasar da aka yi wanda ya sha kayi Shugaba Joe Biden mai jiran gado kuma ya lashe.

“Abinda na ke son yi kenan. Ina so in sami kuri’u 11,780, muna da fiye da hakan a yanzu. Saboda mu muka lashe zabe a jihar.” Abinda Trump ya fada wa Brad Raffensperger babban jami'in zabe, kuma sakataren jam’iyyar Republican na jihar kenan, a wata hira da aka nadi sautinta wadda jaridar Washington Post ta samu ta kuma wallafa ranar Lahadi da rana.

A tattaunawar ta tsawon sa’a daya, a wani lokacin Trump ya matsa wa Raffensperger wani lokacin kuma ya yaba mashi da mai ba ofishinsa shawara, Ryan Germany. Trump dai ya kalubalanci ingancin kidayar kuri’u har sau uku da aka yi a jihar Georgia wanda suka nuna cewa Biden ne dan takarar shugaban kasa daga jam’iyyar Democrat na farko da ya lashe zabe a jihar tun shekarar 1992.

A gefe guda kuma, ‘yan Majalisar Wakilan Amurka daga jam'iyyar Republican fiye da 100 da wasu sanatoci kusan 12, sun ce ranar Laraba zasu goyi bayan kokarin da kusan ba zai yi wani tasiri ba na dakatar da tabbatar da sakamakon kuri’un wakilan zabe wanda ya nuna Joe Biden na jam’iyyar Democrat ne ya kayar da shugaba Donald Trump, a zaben watan Nuwamba.

Tabbatar da sahihancin kuri’un wakilan zabe 306 da Biden ya samu shi kuma Trump ya samu 232 shi ne mataki na karshe kafin a rantsar da Biden a matsayin shugaban Amurka na 46 a ranar 20 ga wannan watan nan na Janairu.

Akwai bukatar dukkan majalisun Amurka 2 su goyi bayan kalubalantar da aka yi kan nasarar da Biden ya samu a zaben kafin a iya sauya sakamakon. ‘Yan Democrat suke da rinjaye a majalisar wakilai, kuma babu shakka zasu tabbatar da nasarar da Biden ya samu, yayin da wasu tsiraru ‘yan Democrat a majalisar dattawa tare da wasu ‘yan Republican da suka amince da nasarar Biden, ta yiwu su yi hakan a majalisar ta dattawan.

XS
SM
MD
LG