Majalisar Dinkin Duniya zata kira taro kan zaman lafiya a Siriya

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon

Majalisar Dinkin Duniya na son ta kira wani taro na musamman dangane da tataunawar samar da zaman lafiya ranar litinin, amma kasancewa ya rage sauran ‘yan kwanakin a yi zaman kuma babu wata yarjejeniyar su wa za su yi zaman, na kawo shakkun cewa ko ma za a yi ganawar bisa lokacin da aka shirya za ‘a yi.

Staffan de Mistura, jakadan Siriya na musamman ya sanar cikin watan da ya gabata cewa yana son su fara ganawa ranar 25 ga watan janairun nan a Geneva.

Jakadan ya sami goyon bayan kasashe 17, ciki har da Amurka, da Rasha, amma har yanzu kasashen ba su yanke shawarar ko wadanne kungiyoyin adawa da ka yaki a Siriya ne za su tura wakilansu wajen zaman.

Mataimakin mai magana da yawun MDD Farhan Haq, ya fada jiya litinin cewa ba a tura gayyata ba tukun har sai an yanke shawarar su wa za su je zaman. Ya kara da cewa har yanzu MDD na na maida hanakali akan ranar ta 25 ta wannan watan ne za’a fara taron kuma sakatare Janar din MDD Ban Ki Moon yana kira ga manyan kasashen duniya da su kara kaimi wajen ganin an cimma yarjejeniya.