Ya sake jaddada goyon bayansa da yunkurin da 'yan Najeriya keyi na tabbatar da cewa an kubutar da 'yan matan Chibok da har yanzu suna hannun 'yan kungiyar Boko Haram ba tare da wani jinkiri ko bata lokaci ba
Mr. Ban Ki-moon yana yin bayani ne bayan kammala ganawa da shugaba Muhammad Buhari inda ya nuna juyayinsa da damuwa akan halin da 'yan matan suke ciki da iyayensu da kuma irin fafitikar da ake yi na cika kwanaki dari biyar da 'yan matan suka yi a hannun 'yan ta'adan.
Yace shi da shugaba Muhammad Buhari sun yi shawarwari akan abubuwa daban daban da suka jibanci tattalin arziki da cigaban jama'a da musabbabin tashin hankalin nan na Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya. Yace na taya Najeriya juyayi da jajintawa akan halin da al'ummar arewa maso gabs suke ciki.
Yace wannan makon shi ne cikon kwanaki dari biyar da 'yan matan suke rike a hannun kungiyar Boko Haram. Yace suna kara jaddada goyon bayansu wajen warware wannan mawuyacin hali da al'umman yankin suke ciki.
Da lafazi mai karfin gaske Mr. Ban Ki-moon ya kira wadanda suka yi danyen aikin su gaggauta sako 'yan matan ba tare da wani sharadi ko bata lokaci ba.
Majalisar Dinkin Duniya da Najeriya zasu dauki duk matakin da ya kamata domin a warware matsalar a cikin dan karamin lokaci.
Ga karin bayani.