Ya bayyana haka ne bayan da ‘yan sanda suka fesa barkonon tsohuwa da yin feshin ruwa ga masu neman mafaka, wadanda suke akan iyakar kasar da Serbia. Yace, ya kadu da ya ga yadda aka yiwa ‘yan gudun hijirar”.
Ya kara da cewa, “wannan baa bin amincewa ba ne, sannan dole a mutunta masu tserewa yaki ko kame a kasashensu.
Shima Firaminstan Serbia Aleksandar Vucic yayi Allah wadai da lamarin da ya kira yanayin rashin tausayi, musamman ga mutanen da ke neman tsira daga masifar yaki a Syria da kasashen Gabas ta Tsakiya.
‘Yan sanda sun kwashe sa’o’i suna artabu da ‘yan gudun hijirar bayan da suka kulle daga daga cikin manyan mashigar Tarayyar Turai.
Hungary tace bakin na kokarin kutsawa karfi da yaji ta shingen kan iyakar ne da ke zame wa kasar hatsari.