Yayi wannan gargadin ne a lokacin ganawarsa da Firayiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a kokarin kwantar da tarzomar kusan makonni uku.
Mista Ban ya kuma ja kunnuwan Israila da Falasdinawa su gujewa hatsarin yaduwar rikicin a addinance da irin illar da hakan zai yiwa yankunan kasashen. Ya kuma yi kira da ayi duk iyakar abun da zai yiwuwa don ganin hakan bata faru ba.
Sakataren ya fadawa manema labarai cewa, yunkurin jami’an tsaron Israila yana iya samun tirjiya, in har basu yi kokarin kashe wutar rikicin kafin mutane su rasa rayukansu ba.
A daya bangaren kuma, a Larabar nan ce ake sa ran Sakataren Wajen Amurka John Kerry zai tashi zuwa Turai da Gabas ta Tsakiya bisa yunkurin taimakawa wajen kashe wutar rikicin Yahudawa da Falasdinawa akalla 50 ne suka hallaka a rikicin.
Sannan zai tuntubi kawayen Amurka a game da maganar tsaro da ya hada da barazanar ISIS da kuma rikicin Syria da Ukraine. Ana sa ran zai gana da takwarorinsa na Saudiyya, Turkiyya, Rasha da Jordan.
Amma karfin ziyarar shine ganawa da Benjamin Netanyahun Isra'ila da Mahmoud Abbas na Falasdinu.