Yau ta ke Ranar mai da hankali kan hanyoyin takaita bala’o’in yau da kullum a duniya. A Jawabinsa kan ranar ta mai da hankali kan bala’o’in da rayuwa ta gada, Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Banki-moon, ya shawarci al’ummar duniya da a rinka ba da muhimmanci ga hanyoyin magance bala’o’i a gargajiyance.
A nasa bayanin, Shugaban Hukumar Ba Da Agajin Gaggawa Ta Kasa Alhaji Alhassan Nuhu ya ce bala’o’in da su ka fi addabar Najeriya sun hada da ambaliyar ruwa da iska da karancin ruwa da dai sauran bala’o’in da rayuwa ta gada da akan fuskanta a sauran kasashen ma. Saidai ya ce Najeriya ba ta taba gamuwa da wasu manyan bala’o’i kamar irirn na tsunami ba.
Shi kuwa wani mazaunin birnin Lagos a Najeriya mai suna Mr. Bolawan Akim ya ce cikin bala’o’in rayuwa da ya fuskanta har da na ambaliyar ruwa, wadda ta auku sanadiyyar yadda mutane ke zuba shara barkatai har ta ke toshe hanyoyin ruwa. Don haka ya yi kira ga hukumomi su dau matakin ganin mutane sun daina zuba shara barkatai da dai sauran abubuwan da ke haddasa matsaloli.
Ga Babangida Jibrin da cikakken rahoton: