ABUJA, NIGERIA - Shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawan ne ya jagoranci zaman majalisar, inda ya karanta bukatun shugaban kasa Mohammadu Buhari akan shirin kasafin kudin badi, da niyyar sa ta nada sabon alkalin-alkalai na kasa, da kokarin biyan wasu basussuka da ake bin kasar, sannan Majalisar ta shiga wani zama na sirri da ya debi sa'o'i uku.
Bayan fitowan su ne Sanata Adamu Bulkachuwa ya yi karin haske akan abubuwan da majalisar ta tattauna akai inda ya ce an duba sha'anin tsaro da nasarar da aka samu.
Amma abinda ya dauki hankali shi ne cewa majalisa ba ta ce komai akan wa'adin da ta ba shugaban kasa Mohammadu Buhari na kawo karshen rashin tsaro ba, wanda ya sa har aka ce idan ba a ga sauyi a harkar tsaron cikin makonni shida ba za a tsige shi, abin tambaya shine ko an gamsu da yanayin tsaro a kasar ne a yanzu.
Sanata Bulkachuwa ya yi bayani cewa sun gamsu da bayanan shugabannin hukumomin tsaro na kasa, domin suna ta taro da su akai akai. Bulkachuwa ya ce majalisar dattawa za ta ci gaba da bibiyan jami'an tsaron akan ayyukan nasu domin kasar ta samu zaman lafiya kafin a kai ga zabe mai zuwa.
To saidai ga Sanata mai wakiltar Taraba ta Kudu Emmanuel Bwacha yana mai ganin akwai abin dubawa baya ga nasarar da aka fara samu a fannin tsaron, inda ya ce lokaci ya kure, kuma ba yanzu aka fara zancen tsige shugaban kasa ba.
Bwacha ya ce kowa yana da hakki akan harkar tsaro a kasar, kuma kowa yana da laifi har su ‘yan majalisar, saboda haka yana ganin akwai aiki a gaba na hada kan kasa da kuma bai wa jami'an tsaro goyon baya saboda a samu nasara mai dorewa.
Daya cikin masu nazari a harkokin mulki da zamantakewa kuma Malami a Jami'ar Abuja Dokta Farouk Bibi Farouk ya yi tsokaci akan batun tsige shugaba Muhammadu Buharin yana cewa fushi ne majalisa ta yi a lokacin da ta bada wa'adin makkwanni shidan, tunda ‘yan majalisa su ne masu yin dokoki, su ne masu sa ido a ayyukan jami'an tsaro, su ne masu kasafta masu kudade.
Farouk ya ce abu ne mai wuya ace majalisa ba ta da laifi, saboda haka yana ganin barazana ce kawai aka yi a batun tsigewar.
Majalisar dattawa ta ba hukumomin tsaro wa'adin makonni biyu , na su gaggauta yin bincike akan harin da aka kai wa abokin aikin su Sanata Ifeanyi Uba a Jihar Anambara, sannan su mika rahoton ga kwamitocin tsaro da leken asiri da na ‘yan sanda na majalisar dattawan.
Saurari cikakken rahoto daga Medina Dauda:
Your browser doesn’t support HTML5