Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Aika Sunayen Sabbin Ministoci Bakwai Majalisar Dattawa


Shugaba Buhari (Facebook/Bashir Ahmad)
Shugaba Buhari (Facebook/Bashir Ahmad)

Mataki na gaba shi ne majalisar za ta saka rana don tantance zabin na Buhari kafin daga bisani a tabbatar musu da mukamansa.

Rahotanni daga Najeriya na cewa, shugaba Muhammadu Buhari ya tura sunayen mutum bakwai Majalsiar Dattawan kasar a matsayin sabbin ministoci.

Manyan kafafen yada kasar sun ruwaito wata wasika da fadar shugaban kasar ta tura a majalisar dauke da sunayen mutanen wadanda za a tantance su kafin tabbatar musu da mukaman.

A ranar 29 ga watan Mayun 2023 wa’adin mulkin Buhari zai kare.

Sunayen mutanen da Buhari ya tura majalisar sun hada da Henry Ikechukwu Iko (Abia) Umar Ibrahim El-Yakub (Kano) da kuma Joseph Ukama (Ebonyi.)

Sauran sun hada da Umana Okon Umana (Akwa Ibom) Adewole Adegoroye (Ondo) Odum Udi (Rivers) da Goodluck Nnana Opia (Imo.)

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, babu karin bayani kan ma’aikatun da za a ba kowane daga cikinsu.

Mataki na gaba shi ne majalisar za ta saka rana don tantance zabin na Buhari kafin daga bisani a tabbatar musu da mukamansa.

Saurari cikakken rahoton Medina Dauda daga Abuja:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:41 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG