Mahaukaciyar Guguwar Beryl Ta Yi Barna A Kudu Maso Gabashin Caribbean

Mahaukaciyar Guguwa Beryl

Guguwar Beryl ta ratsa kan ruwa a ranar Talata a matsayin wata mummunar guguwa mai rukuni 5 a kan hanyar da za ta bi kusa da Jamaica da tsibirin Cayman bayan da ta afkawa yankin kudu maso gabashin Caribbean, inda ta kashe akalla mutane biyu.

An bada gargadin guguwa ga Jamaica da kuma tsammanin guguwar ta isa Grand Cayman, da Little Cayman da Cayman Brac.

An yi hasashen karfin Beryl ta ragu a ranar Talata amma har yanzu tana dauke da karfi lokacin da za ta wuce kusa da Jamaica ranar Laraba, tsibirin Cayman a ranar Alhamis da tsibirin Yucatan na Mexico a ranar Juma'a, a cewar Cibiyar Guguwa ta kasa.

Beryl ita ce guguwar farko ta rukuni 5 da ta taɓa tasowa a cikin Tekun Atlantika, wanda ruwan dumi ya rura ta.

Da sanyin safiyar Talata, guguwar ta kasance a nisan mil 370 (kilomita 595) kudu maso gabas da Isla Beata a Jamhuriyar Dominican. Tana dauke da iska mai karfi na 165 mph (270 kph) kuma tana ratsawa ta yamma-arewa maso yamma a 22 mph (35 kph).

"Beryl dai ta kasance mahaukaciyar guguwa ta 5 mai ban mamaki," in ji Cibiyar Guguwa ta kasa.

An bada gargadin guguwa ga daukacin gabar tekun kudancin Hispaniola, tsibirin da Haiti da Jamhuriyar Dominican suka raba.

-AP