Mafarauta Zasu Shiga Dajin Sambisa Su Kakkabe 'Yan Boko Haram

Mafarauta

Kungiyar mafarauta tana bukatar gwamnati ta janye sojoji daga dajin Sambisa kana su shiga su kakkabe 'yan kungiyar Boko Haram dake rike da 'yan matan Chibok.
Mai magana da yawun kungiyar mafarauta yace daji baya basu tsoro domin duk wani gari maharbi ne ya kafa shi.

Lokacin da babu soja kuma babu 'yan sanda maharbi shi ne mai tsaron gari. Yace 'ya'yansu aka kama kuma an ajiyesu a daji wurin da su maharba ke takama dashi. Sabili da haka su maharba suna rokon gwamnati ta basu izinin shiga dajin. Amma gwamnati ta janye sojoji domin su san babu wani a dajin sai 'yan kungiyar Boko Haram.

Dangane da ko yaya zasu iya tunkarar masu bindigogin zamani hade da tankoki da nasu kwari da baka da bindigogin harbi ka ruga, sai yace taimako daga Allah yake. Yace Allah zai taimakesu akan 'yan Boko Haram. Abun da suke so kawai shi ne su samu tabbacin cewa babu kowa a dajin sai 'yan kungiyar.

Game da lokacin da zai daukesu su kawar da 'yan ta'adan sai yace hikimar yadda zasu shiga daji da abubuwan da zasu yi wanna kuma nasu ne na mafarauta. Amma ba zasu sa ranakun da zasu yi ba. Wannan kuma yana hannun Allah.

Akan ko suna ganin gwamnati ta gaza sai yace gwamnati bata gaza ba. Tana iyakar kokarinta. Amma abun ya dagula masu kai. Yanzu suna son su kawo nasu taimako. Yace suna ganin zasu iya yin abun a cikin lokaci ba kamar yadda gwamnati ke yi ba.

Ga rahoto.

Your browser doesn’t support HTML5

Idan Sun Samu Izin Mafarauta Zasu Kakkabe Boko Haram Daga Dajin Sambisa - 1'53"