A wani mataki na kokarin aiwatar da umarnin da Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar na a fara sayarwa da matatun man cikin gida man fetur a naira, ma’aikatar kudi da kamfanin man kasa na NNPCL sun fara zama a ranar Laraba a Abuja.
A karshen watan Yuli Tinubu ya ba da umarni ga kamfanin na NNPCL da ya fara sayarwa da ‘yan kasuwar cikin gida mai a naira, a wani mataki na sauke farashin man.
Ministan kudi da tattalin arziki Mr. Wale Edun ya gana da masu ruwa da tsaki a ofishinsa da ke Abuja a wani yunkurin na ganin an aiwatar da wannan umarni.
Daga cikin mahalarta taron har da shugaban kamfanin man na NNPCL, Mele Kyari da Ministan albarkatun mai, Mr Heineken Lokpobiri.
Kwararru a fannin tattalin arziki sun ce daukan wannan mataki zai taimaka matuka wajen rage hauhawar farashin mai.