Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Kaddamar Da Ayyukan Samar Da Iskar Gas Uku  


Lokacin Da Gwamnatin Najeriya Ta Kaddamar Da Ayyukan Iskar Gas Uku
Lokacin Da Gwamnatin Najeriya Ta Kaddamar Da Ayyukan Iskar Gas Uku

A daidai lokacin da duniya ke komawa fannin amfani da iskar gas don rage illolin sauyin yanayi ga al’umma, gwamnatin Najeriya ta kaddamar da muhimman ayyukan samar da iskar gas guda uku a jihohin Imo da Delta.

Ana ganin hakan zai taimaka wajen rage dogaro ga man fetur kacokan tare da habbaka tattalin arzikin kasar.

Masu Ruwa Da Tsaki Da Suka Halarci Taron Kaddamar Da Ayyukan Iskar Gas Uku
Masu Ruwa Da Tsaki Da Suka Halarci Taron Kaddamar Da Ayyukan Iskar Gas Uku

Kamfanin kasuwancin man fetur na Najeriya wato NNPCL ne ya jagoranci aikin samar da iskar gas na gwamnatin Najeriyar a kananan hukumomin Assa ta arewa da Ohaji ta kudu na jihar Imo wanda ya ratsa tare da wuce cikin jihar Ribas, aikin da kaurin bututun sa ya kai inchi 36 kuma tsawon kilomita 23.3, sannan da aikin yankin Kwale na jihar Delta.

Wannan aikin dai ya kunshi tsarawa, ginawa da kuma sayen kayayyakin shi wanda zai rika samar da Cubic Feet na iskar gas miliyan 300 a kowacce rana kama daga injin sarrafawa da adana gas, bututu biyu, motocin dako da kuma ofishin kula da muhimman ayyukan rarrabawa na yankunan da ake aikin don amfanar dukkan ‘yan kasa.

Mele Ya Yi Bayani Akan Kaddamar Da Ayyukan Iskar Gas Uku Don Habbaka Tattalin Arziki
Mele Ya Yi Bayani Akan Kaddamar Da Ayyukan Iskar Gas Uku Don Habbaka Tattalin Arziki

A yayin kaddamar da aikin, shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya ta ya tawagar dake gudanar da aikin na kamfanin NNPCL da saura masu ruwa da tsaki murna a kan gagarumin kokarin da suka yi don ci gaban kasa a cikin kasa da shekaru biyu wato watannin 11 kamar yadda suka yi alkawari.

Yana mai cewa wadannan ayyukan na da mahimmancin gaske ga Najeriya kuma ya ce gwamnati zata kara ninka kokarin ta wajen tabbatar da raya fannin samar da iskar gas wanda zai taimaka wajen rarraba makamashi, bunkasa ci gaban masana’antu, samar ayyukan yi, bunkasa tattalin arziki da saura ababen ci gaba a kasa.

Taron Gwamnatin Najeriya Na Kaddamar Da Ayyukan Iskar Gas Uku Don Habbaka Tattalin Arziki
Taron Gwamnatin Najeriya Na Kaddamar Da Ayyukan Iskar Gas Uku Don Habbaka Tattalin Arziki

Ko yaya aka kai ga wannan matsayi na kaddamar da aikin a cikin watanni 11 a maimakon shekara biyu da aka tsara tun farko: shugaban kamfanin NNPCL, Mallam Mele Kyari, ya bayyana cewa sun kara yawan ma’aikata dake gudanar da aiki tare da karfafawa wadanda aka bai wa kwangila har ya kai ga samun wannan nasara.

Babban daraktan kamfanin AGPC, daya daga cikin masu ruwa da tsakin dake gudanar da aikin, Effiong Okon ya ce kaddamar da aikin gaggarumar nasara ce ganin yadda akwai wadataccen iskar gas da za ta taimaka wajen samar da wutar lantarki ga kasar baki daya baya ga aikin sarrafa takin noma na zamani, da fitar da iskar gas din kasashen waje gwamnati sami kudadden shiga.

Lokacin Taron Gwamnatin Najeriya Na Kaddamar Da Ayyukan Iskar Gas Uku Don Habbaka Tattalin Arziki
Lokacin Taron Gwamnatin Najeriya Na Kaddamar Da Ayyukan Iskar Gas Uku Don Habbaka Tattalin Arziki

Ya kuma kara da cewa, abun alfahari ne yadda aka ga ci gaba a aikin da kamfanonin NNPCL da SEPLAT wadanda suka hada karfi da karfe wajen zuba jarin ci gaba da aikin da aka kaddamar kuma da yardar Allah za’a fara samar da iskar gas don amfanin al’umma zuwa zango na uku na shekarar nan.

Haka kuma, shugaban kamfanin NNPCL, Mallam Mele Kyari, ya fayyace ma manema labarai fa’idar aikin da aka kaddamar a jihohin Imo da Delta, ya ce samar da gas a kasa zai inganta fannin wutar lantarki baya ga samun taki da saura muhimman abubuwan makamashi.

Ko yaya za’a iya rarraba iskar gas din nan idan aka samar, Mallam Mele Kyari ya ce NNPCL ya fara samar da fanonnin a kusan dukkan gidajen man kamfanin dake fadin kasar don saukake aikin.

Taron Kaddamar Da Ayyukan Iskar Gas Uku Don Habbaka Tattalin Arziki
Taron Kaddamar Da Ayyukan Iskar Gas Uku Don Habbaka Tattalin Arziki

Idan ana iya tunawa, a kusan watanni 11 da suka gabata, shugaban Najeriya ya sanar da cewa gwamnatinsa zata bada karfi wajen karkatar da akalar tattalin arzikin kasar zuwa ga fannin iskar gas kuma tuni ya kaddamar da wani shiri mai suna PCNGi wato Presidential CNG initiative.

A yau Laraba ne gwamnatin tarayya ta bayyana wasu jerin ayyuka da za su kai ga shirin rarraba motocin bas masu amfani da iskar gas karkashin wani shiri na shugaban kasa a fadin kasar domin fara maye gurbin masu amfani da man fetur da za a kaddamar a ranar 29 ga watan Mayu lokacin da zai cika shekara 1 a kan karagar mulki.

Saurari cikakken rahoto daga Halima Abdulrauf:

Gwamnatin Najeriya Ta Kaddamar Da Ayyukan Iskar Gas Uku Don Habbaka Tattalin Arziki .mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:57 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG