Likitoci Musulmi 'Yan Najeriya Daga Kasar Ingila Sun Kawo Dauki Arewa Maso Gabas

Wata tawagar Likitoci daga kasar Ingila, ta kungiyar Musulmi ‘yan Najeriya karhashin jagorancin Dr. Muhammad Ibrahim Sadiq, wanda ya kasance dan asalin yanke ne sun kawo taimako ga alumar jihar Taraba.

Tawagar Likitocin sun fara yada zango ne a babban Asibitin garin Gembu, dake karamar hukumar Sardauna, dan duba marasa lafiya da kuma bada magunguna, inda suke kwashe kwanaki biyu a garin suna duba lafiyar jama’a, bisa cututtukan yara da manya maza da mata har da masu cutar ido.

Dr. Muhammad Ibrahim Sadiq, yace kungiyar tayi irin wannan aiki a jihohi kamar jihar Kano jihar Katsina, jihar Zamfara da jihar Sokoto amma wannan shine karo su na farko a arewa maso gabashin Najeriya.

Ya kara da cewa sun zabi garin Gembu ne saboda yana daya daga cikin garuruwan Najeriya, da yake da nisansa daga koina sai an wahala akan zo garin kuma basu da wani ingantatcen Asibiti kuma ga jama’a da cututtuka iri iri.

Mutanen garin sun nuna godiya ga Likitocin da kuma kira ga sauran ‘ya’yan su dake kasashen waje dasu kwaikwai abunda Dr. Muhammad da tawagar sa suka yi na taimakawa jama’ar jihar.