An gano cewar, yara da ake haihuwa da renonsu har zuwa munzilin girmansu a yanayi na hayaniya. Suna samun matsala da take shafar yaruntar su, da zama ummul haba-isin matsalar fahimtar karatunsu idan sunkai muzulin karata.
A wani bincike da aka gudanar a jami’ar Arewa masoyamma tanan kasar Amrka, an bayyanar da cewar kwakwalwar yara daga kimanin haihuwa, zuwa shekaru uku 3 nada wasu jijiyoyi a kwakwalwarsu da basu da karfi, wanda tahaka idan suna fuskantar hayaniya, to sukan iya toshewa, ta yadda yara na iya fuskantar mawuyacin hali a wajen koyon karatu bayan sun girma.
Sun kara dacewar idan har yaro zai iya fahimtar bakakke kuma akwai hayaniya a wannan yanayin to lallai bashakka wadannan yaran bazasu samu tirjiyaba wajen fahimtar karatu ba.
A tabakin babbar mai gudanar da wannan bincikin Nina Kraus, tace, “Idan kusan kunada yara ‘yan shekaru 3 to lallai yazama wajibi a gareku ku kokarta sama musu yanayi maras hayaniya, don kubutar dasu daga wanna mummunan hadarin”