Mai rikon kwarya hukumar zaben Najeriya, Hajiya Amina Zakari, ta kara fayace manufofin aikin ta da tace zata karfafa anfani da naurar tantance masu kada kuri’a, da yaki da wadanda suke yunkurin magudi a zabubbukan cike gurbi na dan majalisar tarayya da za’a yi a Katsina a watan gobe da zaben Gwamnoni jihar Kogi da Bayelsa, a watan Nuwamba da Disambar bana nan.
Amina Zakari, dake Magana a zauren tara rahotanin zaben 2015, na kungiyoyi masu zaman kansu tace tabbas za’a kara ganin sauyi a aikin hukumar a wadannan zabubbuka.
Tuni jamiyyar adawa ta PDP, ta nuna rashin amincewa da nadin Amina Zakari, tayi rikon kwarya hukumar, da nuna cewa Gwamnatin APC, ta nada tane dan kwacewa PDP, jihohin Kogi, da Bayelsa.
Sam baza mu yarda da yadda APC, ke yunkurin maida Najeriya, kasa mai bin jami’yyar siyasa day aba inji kakkakin PDP, Oliseh Metu, wanda yace ba zasu amince da jagorancin Amina Zakari ba.
Inda hakan ke nuni da cewa ko PDP, taki shiga zaben ko kuwa idan bata samu nasarar ci gaba da Gwamnonin ta Idris Wada a Kogi, da Dickson a Bayelsa, tayiu watsi da sakamakon zaben.