Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matsalar Hanya na Neman Maida Hannun Agogo Baya a Arewa Maso Gabas


Yayin da al’ummomin yankunan da aka kwato daga hannun mayakan Boko Haram ke cigaba da komawa,a arewacin jihar Adamawa,yanzu haka wata ta kunno game da matsalar rashin hanya sakamon rashin gyara gadojin da aka rusa da boma-bomai, a kananan hukumomin Michika da Madagali.

Wannan matsalar dai yanzu haka na neman mai da hannun agogo baya,yayin da kuma al’ummomin da suka bi ta barauniyar hanya suka koma ke fama da matsalar rashin cimaka,da rashin likitoci da kuma cibiyoyin shan magani,lamarin da ya kai wasu sake komawa gudun hijira.

Wadannan gadoji dai sune mahada tsakanin al’umomin da wasu yankunan jihar Adamawa, sai dai kuma yayi da al’umomin ke fama da wadannan matsaloli, hukumomi a jihar Adamawa, na kokarin ganin cewa an magance matsalolin da al’umomin ke fama dashi.

XS
SM
MD
LG