Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alherin Ziyarar Shugaba Buhari Amrka ga Matasa


Sahabo Imam Yana Tattaunawa da shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya a Balir House.
Sahabo Imam Yana Tattaunawa da shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya a Balir House.

A yayinda shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya kamala ziyararsa ta kwanaki uku a nan kasar Amrka, matasa da yawa a ciki da wajen kasar na ta bayyanar da ra’ayinsu dangane da wannan ziyarar. A tabaki wasu da muka zanta dasu, sun yimuna bayanin dangane da ra’ayoyinsu a kan wanna ziyarar.

Suna ganin cewar yakamata ace duk abubuwan da aka tattauna na cigaban kasa, a wannan tafiya to yakamata lallai a aiwatar dasu a aikace ba kawai su zauna a takardaba, kana shi shugaba Buhari, ya bada kaimi wajen ganin an dawo da wadannan kudaden da aka sace, wanda su ne sukasa talauci yayi yawa a cikin al’uma. Kana kuma a san dacewar babban abun da yake haifar da wanna aikin na ta’addancin boko haram ba wani abu bane, illa talauci da rashin aikinyi ga matasa, babu shakka idan aka magance wadannan matsalolin za’asamu zaman lafiya a kasar baki daya. Domin rashin aikinyin ne ake amfani dashi wajen jawo hankalin wadannan matasa a sasu cikin wadannan munanan aiyukan.

Suna ganin cewar idan akayi kokarin ganin duk wata ma’aikata sunbi doka da oda wajen gudanar da ayyukansu, to shima zai taimaka matuka wajen dawo da kwanciyar hankali a kasar baki daya. Sai kuma al’umar kasar su taya shugaban da addu’ar Allah yabashi nasara wajen gudanar da aikin shi cikin gaskiya da adalci.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG