Liverpool Ta Kai Zagayen ‘Yan 16 A Gasar Europa League

Liverpool a gasar Europa League

Liverpool ta fara ganin gabanta ne bayan da Luis Diaz da Cody Gakpo suka fara zura mata kwallaye a wasan da aka tashi da ci 4-0 da LASK ta kasar Austria.

Kungiyar Liverpool ta kasar Ingila ta samu kai wa zagayen ‘yan 16 a gasar Europa League.

Liverpool ta fara ganin gabanta ne bayan da Luis Diaz da Cody Gakpo suka fara zura mata kwallaye a wasan da aka tashi da ci 4-0 da LASK ta kasar Austria.

Leverkusen ta ci gaba da kasancewa kungiyar da ke da samun nasara bayan wasanni biyar bayan nasarar ci 2-0 da ta samu a hacken a rukuin H.

Ita ma Atlanta ta kai zagayen na ‘yan 16 duk da kunnen doki da suka yi da Sporting Lisbon a gida da ci 1-1.

Shi kuwa Tomas Soucek ya samu kwallon da ya doka a ragar TSC Back Topol, lamarin da ya ba West Ham damar zuwa zagayen na ‘yan 16.

Ita ma Brighton ta kai zagayen na ‘yan 16 a rukunin B inda ta lallasa AEK da ta buga wasan da ‘yan wasa 10 a Athens.