Kwallon da Darwin Nunez ya zura da wacce Mohamed Salah ya ci, biyo bayan kuskuren da Thibaut Courtios ya yi na bashi kwallo ya bai wa Reds nasara da ci 2-0 a minti na 14 kacal a fafatarwar da suka yi a wasan farko na zagayen ‘yan 16 a ranar Talata.
Hakan ya nuna cewa akwai sauran rina a kaba, yayin da masu rike da kofin suka farfado a karawar da suka yi a wasan karshe na bara, inda Vinicius ya farke kwallo daya kafin wani mummunan kuskure da Alisson ya yi da ya bashi dama zura kwallo ta biyu a rabin lokacin na farko.
Eder Militao ne ya zura kwallo ta uku a farkon rabin lokacin na biyu kafin Benzema ya zura kwallaye biyu da suka bai wa bangaren Carlos Ancelotti dama a wasan da za su yi na biyu a babban birnin kasar Sipaniya a ranar 15 ga watan Maris.
Los Blancos sun kasance a gaba mintuna biyu da shiga rabin lokaci na biyu, ko da yake, lokacin da ‘yan bayan ba su kula da Militao ba da ya zura kwallo da ka yayin da Luka Modric ya dauko firikik.
Wani maraice da aka fara da kyau daga baya ya daukar wani sabon salo mai muni ga Liverpool, inda Benzema ya buga kwallo da karfi ta bugi Joe Gomez sannan ya bai wa Alisson kafa.
Liverpool ta bada wata dama da ta sake budawa bayan minituna 67, Modric da Vinicius sun yi musayar kwallo kafin Benzema ya zaunar da Alisson kana ya nuna nutusuwa ya zura kwallon da kafar hagu.
Wannan ne karon farko da Liverpool ta sha kashi a gida a tarihin gasar zakarun Turai, inda ta yi rashin nasara da ci 3-0 a shekarar 2014.