A taron manema labaran da suka kira, kwararrun likitoci magoya bayan kungiyar ‘SMES’ sun yi tir da abin da suka kira take-taken hukumomin kiwon lafiya sakamakon tursasawar da suka ce ana yi wa abokan aikinsu a nan Nijar kamar yadda abin ya faru a baya -ayan nan da wata kwararriyar likitar cutar daji, Dr. Dille Issimouha.
Dr. Nafissa Naneito kusa ce a kungiyar kwararrun likitocin, ta kuma ce ana kumbiya-kumbiya wajen fitar da kudaden da ake biya da ake fitar da marasa lafiya ‘yan Nijar kasar waje domin neman magani.
Sakataren Kungiyar ta SMES, Dr. Zabeirou Kongouize, ya ce tuni dai kungiyar ta shigar da kara a gaban hukumar yaki da cin hanci ta HALCIA domin ta binciki wannan al’amari.
A karon farko, tun bayan tasowar wannan takaddama, ofishin Ministan Kiwon Lafiyar Al’umma, ya maida martani ta hanyar taron manema labaran da Magatakardan Ministan, Abache Ranao, ya kira a jiya Laraba.
Yanzu dai hankalin ‘yan Nijar ya karkata wajen hukumar yaki da cin hanci ta HALCIA domin jin abubuwan da rahoton bincikenta zai kunsa.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma daga Yamai:
Your browser doesn’t support HTML5