A jamhuriyar Nijar wasu mata sun yi zaman dirshan jiya lahdi a harabar babban Asibitin birnin Yamai da nufin nuna rashin amincewa matakin dakatar da wata kwarariyar likitar Cutar Daji Dakta Dille Issimouha daga aiki, bayan da ta fallasa wasu bayanan sashen kula da aiki.
Matan wadanda yawansu ya doshi 100 galibinsu wadanda ke fama ne da cutar daji, na cewa dakatar da wannan kwararriyar likita daga aiki tamkar mayar da hannun agogo baya ne, a yakin da hukumomin Nijar suka kaddamar da cutar Daji.
Dakta Dille Issoumouha na daya daga cikin likitoci 2 kacal da ke kula da masu fama da cutar Cancer a wannan kasa. A shekarun baya ta yi watsi da tayin wata asibitin kwararru dake kasar Senegal, inji mahaifiyarta wacce ta halarci wannan gangami.
Da yake bayani akan wannan gangamin Darektan babban asibitin Yamai Gagara Dalla ya bayyana cewa ba a saba ka’ida ba wajen korar wannan mata daga aiki.
A watan jiya Dakta Dille Issoumaha wace ke shugabantar wata kungiyar yaki da cutar Cancer ta gwadawa manema labarai wasu takardun dake nunin yadda jami’ai ke cire miliyan 16 na cfa daga aljihun gwamnati.
Ga saurari cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.
Facebook Forum