A jamhuriyar Nijar ambaliyar ruwa a sakamakon cikar kogin Komadougou, ya tilastawa dubban mutanen jihar Diffa kaura daga gidajensu, inda rikicin Boko Haram ya haddasa koma bayan tattalin arziki a yankin na manoma da makiyaya da kuma masu kamun kifi a matsayin madogararsu. Al'amarin da ya sa ‘yan Majalisar Dokokin yankin suka fara neman a tallafa wa wadanda wannan bala’i ya rusa da su.
A taron manema labarai da suka kira a birnin Yamai, wakilan al’umar Diffa a Majalisar Dokokin kasa sun nuna damuwa akan dimbin asarar dukiyoyin da kogin na Komadougou ya haddasa tare da tilastawa mazaunan wasu manyan garuruwan yankin ficewa daga matsugunnansu.
Yankin Diffa mai makwaftaka da kasashen Chadi da Najeriya na fama da matsaloli masu nasaba da rikicin Boko Haram, yau shekaru kusan hudu, lamarin da ya hana wa jama’a gudanar da aiyukan da mutanen yankin ke dogaro akansu.
A saurari cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.
Facebook Forum