Wannan shawarar na kunshe ne a cikin karar da lauyoyin suka gabatarwa kotu kafin a yanke masa hukunci a mako mai zuwa a New York.
Cohen ya amince da laifinsa na aikata ba daidai ba kuma ya baiwa binciken da hukumomin jiha da na tarayya suka gudanar watanni da watanni hadin kai, ciki har da ganawa sau bakwai da ya yi da mai bincike na musamman Robert Muller.
Masu shigar da karar sun ce sashen kimanta hukunci na kotu, yace tsarin tabbatar da hukuncin tarayya ya nuna Cohen zai iya zaman akalla shekaru hudu a gidan yari. Lauyoyin gwamnatin sun ce kiyasin hukuncin na tabbatar da girmar laifin da Cohen ya aikata cikin ganganci.
Masu shigar da karar sun ce bai kamaci a yiwa Cohen sassaucin da aka saba yiwa wadanda suka baiwa bincike hadin kai ba, yayin da suke bada dalilansu bisa amincewarsa.