Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Da China Sun Kulla Sabuwar Yarjejeniyar Cinikayya


Shugabannin Amurka da na China
Shugabannin Amurka da na China

Jiya Litinin shugaban Amurka Donald Trump ya nuna fariya kan dangantakarsa mai karfin gaske da shugaban kasar China Xi Jinping, inda ya bayyana wata sabuwar yarjejeniyar cinikayya tsakanin Amurka da China, wadda zata baiwa manoman Amurka damar sayar da kayayyakin da suke nomawa ga Beijing.

Kasuwannin hannun jari a Asiya da Turai sun yi tashin gwauran zabi, bayan tattaunawar Trump da Xi wadanda suke zaman shugabannin kasashe biyu da suka fi girman tattalin arziki a duniya. Sun amince ranar Asabar a Argentina cewa babu wata kasa da zata kara sakawa wata haraji kan kayayyakin da suke fitarwa, har tsawon kwanaki 90, yayin da zasu ci gaba da tattaunawa kan bayanan yarjejeniyar cinikayya.

Kasuwar hannun jari ta Amurka, ta bude cikin sa a farkon wannan makon.

Mai baiwa shugaban Amurka shawara kan tattalin arziki, Larry Kudlow, ya ce China ta yiwa Amurka alkawarin sayen kayayyakin da ake kerawa a Amurka na sama da dala Triliyan daya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG