Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Comey Ya Amsa Gayyatar 'Yan Republican a Majalisa

Tsohon Darektan Hukumar binciken manyan laifuka ta FBI a Amurka, James Comey
Tsohon Darektan Hukumar binciken manyan laifuka ta FBI a Amurka, James Comey

A watan da ya gabata, kwamitin da ke bincike, ya aikawa da Comey takardar gayyata kan binciken da ake yi game da zargin alaka tsakanin gangamin yakin neman zaben Donald Trump da Rasha da kuma batun sakonnin email din Hillary Clinton.

A yau Juma’a, ‘Yan majalisar wakilai a bangaren jam’iyyar Republican, suna yi wa tsohon shugaban hukumar binciken manyan laifuka ta FBI James Comey tambayoyi.

Wannan zangon tambyoyin, wanda za a yi shi cikin sirri, zai kasance shi ne karshe, kafin ‘yan Republican din su mika ragamar jagorancin majalisar ga ‘yan Democrat. A watan Janairu badi.

A watan da ya gabata, kwamitin da ke bincike, ya aikawa da Comey takardar gayyata kan binciken da ake yi game da zargin alaka tsakanin gangamin yakin neman zaben Donald Trump da Rasha da kuma batun sakonnin email din Hillary Clinton.

Da farko Comey ya bayyana cewa ba zai amince ya bayyana a gaban kwamitin ba, idan dai a boye za a yi mai tambayoyin.

Amma ya amince daga karshe, bayan da aka yi mai alkawarin cewa za fitar da takardar duk abin da aka tattauna ga jama’a sa’ao’I 24 bayan kammala ganawar.

Su dai ‘yan majalisar dokoki na bangaren ‘Yan Republican, na zargin cewa, kin jinin Trump da wasu manyan jami’an gwamanti ke yi, shi ya kai ga aka hukumar ta FBI ta mayar da hankalinta kan binciken alakar gangamin yakin neman zaben Trump da Rasha, suna masu jaddada cewa hukumar ta ki mayar da hankali kan binciken batun sakonnin email din Hillary Clinton.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG