A yau Labara ne tsofaffin shuwagabbani Amurku guda hudu tare da mai ci yanzu, zasu taru domin kai ziyarar bankwana ga tsohon shugaba kasar Amurka, George Herbert Walker Bush, babba shugaban kasar Amurka na 41, wanda ya mutu a ranar Juma’ar da ta gabata yana da shekaru 94 a duniya.
A ciki harda tsohon shugaba Jimmy Carter, Bill Clinton, Barak Obama inda zasu hadu da Shugaba Donald Trump, don nuna alhininsu ga mamancin tsohon Shugaban, a babbar cocin kasa dake birnin Wahington DC.
Inda zasu saurari jawabin dan marigayi shugaba Bush karami wanda shine shugaban Amurka na 43.
Har ila yau wadanda zasu yi jawabai sun hada da tsohon Firai Minista Brain Mulroney na kasar Canada, sai tshohon Sanatan Amurka Alan Simpson. Tare da shaharraren masanin tarihi Jon Meacham, babban marubucin tarihin mamacin shugaba Bush babba.
Daga cikin jiga-jigan da zasu halarci jana’izar sun hada da Yarima Charles na kasar Burtaniya, sai shugabar Jamus Angela Merkel, da Lech Walesa, tsohon shugaban kasar Polnad.
Facebook Forum