Lauya Mai Matukar Tsoron Matar Sa

FILE - Security workers do a last inspection of the War Crimes Court room before the inauguration ceremony of the Bosnian War Crimes Court, in Sarajevo, March 9, 2005.

Wani Lauya mai kare mai lefi a birnin Pittsburgh dake jihar Pennsylvania, ya nemi a ‘dage zaman kotun da aka shirya yi domin tsoron matar sa da yake, a inda yayi ta rokon alkali da ya dage karan domin matar sa na nakuda zata haihu, kuma lamari ne na rayuwa ko mutuwa kasancewar idan har ya zauna kotu har ta haihu baya gurin to tabbas kwananshi ya kare domin zata kasheshi.

Rahotanni sun nuna cewa mai shari’a ya amince da wannan bukata ta wannan Lauya, duk da yake dalilin nasa wani abune da ba’a saba gani ba a dakin shari’a.

Shidai lauyan mai suna Daffner yace lauya mai gabatar da kara da Alkali sun amince da ‘daga zaman kotun, ana dai tuhumar wandan yake karewa da laifin karbar kayan sata.

Ya cigaba da cewa nasan bani da wani kwakwkwaran dalili da zai sa a dage karan, amma gaskiya ne.

Har yanzu dai ba’a tabbatar da cewa ko matar tasa ta sauka ba ko tukunna.